Gwamnatin Jihar Kaduna ta musanta rahotannin da ke cewa, ‘yan fashin daji sun kai hare-hare tare da taimakon wani jirgi mai saukar ungulu, tana mai tabbatar da mutuwar mutum 32.
Tun farko shugaban ƙungiyar tuntuɓa ta ‘yan ƙabilar Adara (ADA) da kuma mai magana da yawun shugaban ƙungiyar mazauna Kudancin Kaduna ta SOKAPU sun faɗa cikin wata sanarwa cewa wani jirgin helikwafta ne ya taimaka wa ‘yan fashin dajin yayin hare-haren. In ji BBC.
Sai dai cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis, Kwamashinan Tsaro Samuel Aruwan ya musanta rahoton yana mai cewa, jirgin da aka gani na rundunar sojan Najeriya ne da ya kai ɗauki wurin.
Sai dai kwamashinan ya tabbatar da kashe mutum 31 a garuruwan Dogon Noma da Unguwan Sarki, sannan maharan suka kashe mutum ɗaya a Unguwan Maikori tare da ƙona gidaje a ranar Lahadi da ta wuce.
“Zuwan jirgin soja na rundunar Operation Whirl Punch ne ya daƙile yunƙurin ‘yan fashin bayan sun kashe mutum ɗaya tare da ƙona gidaje. Saboda haka labarin cewa jirgi ya taimaka wa ‘yan fashi ba gaskiya ba ne,” a cewarsa.
Kazalika, kwamashinan ya nemi waɗanda suke iƙirarin da su kawo wa gwamnati “hujjar yankan shakku”.