fidelitybank

Jirgin sama ya yi hadari a Kamaru

Date:

Ma’aikatar kula da harkokin sufuri a Kamaru ta ce, wani karamin jirgin saman fasinja da ke ɗauke da mutum 11 ya yi hadari a wani daji da ke kudu da Yaounde babban birnin Kamaru a jiya Laraba.

Har yanzu ba a san musababbanin abin da ya haddasa hadarin ba, to amma rahotannin sun ce sadarwa ta katse tsakanin filin jirgin da kuma matuƙan jirgin.

Daga bisani an gano shi a kusa da wani daji da ke kusa da Nanga Eboko da ke da nisan kilomita 150 daga Yaounde.

Jirgin ya tashi ne daga filin jirgin saman Nsimalen zuwa Belabo da ke gabashin kasar in ji ma’aikatar sufurin.

Kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ruwaito cewa wani kafanin Mai mai zaman kansa mai suna COTCO ne ya yi shatar jirgin.

Wannan ne dai karo na farko da aka samu babban hadarin jirgin sama a kasar tun shekarar 2007, a lokacin da jirgin saman Kenya dauke d afasinjoji 114 ya yi hadari jim kadan bayan ya tashi da ga Douala.

www.legit.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp