fidelitybank

Jirgin sama ya lakume rayuka 68 a Nepal

Date:

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Nepal, ta bayyana cewa akalla mutane 68 ne suka mutu a jiya Lahadi, lokacin da wani jirgin cikin gida ya yi hatsari a yankin Pokhara.

Muryar Amurka ta bayar da rahoton cewa, hatsarin a cewar hukumomi a kasar Nepal, shi ne hatsarin jirgin sama mafi muni cikin shekaru 30 da aka yi a karamar hukumar Himalaya.

Ma’aikatan ceto da dama na kasar Nepal na lekowa a gefen tuddan da jirgin Yeti Airlines dauke da mutane 72 daga Kathmandu babban birnin kasar ya sauka.

Talabijin na cikin gida ya nuna ma’aikatan ceto suna ta zagaya sassan jirgin da suka karye inda wasu daga cikin kasa da ke kusa da wurin da hadarin ya faru ya kone, tare da ganin lasar wuta.

Tashar yanar gizo ta Safety Network ta nuna cewa hatsarin shi ne mafi muni a Nepal tun shekarar 1992, lokacin da wani jirgin saman Pakistan Airbus A300 ya yi hadari a wani tsauni a kan hanyarsa ta zuwa Kathmandu, inda ya kashe dukkan mutane 167 da ke cikinsa.

general news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp