fidelitybank

Jirgin sama na Nigeria Air zai iso Najeriya ranar Juma’a – Sirika

Date:

Ministan sufuri na ƙasa, Sanata Hadi Sirika, ya bayyana cewa jirgin saman kamfanin Nigeria Air zai isa ƙasar nan ranar Juma’a wani lamari da zai zama babban ci gaba ga shirye-shiryen soma tafiyar da harkokin kamfanin.

A hirar da ya yi da gidan Talabijin na Channels, ministan ya ce jirgin zai isa ƙasar ne cikin kwana biyu.

Ya yi alƙawarin cewa za a ƙaddamar da jirgin mai kalolin tutar Najeriya domin cika duka alƙawuran da gwamnatinsu ta yi a ɓangaren sufuri.

Sai dai ya ce abin da ya rage kaɗai shi ne samar unguwanni kusa da filin jirgin sama wanda zuwa yanzu an kai kashi 60 cikin 100 na aikin.

A cewarsa, an kammala iza tubalin ginin kuma suna neman gwamnati mai zuwa ta ƙarasa aikin samar da unguwannin ta yadda zai sauƙaƙa wa mutane hawa jirgin.

Sirika a cikin watan Maris, yayin wani taron masu ruwa da tsaki a ɓangaren sufuri, ya ce kamfanin Nigeria Air zai soma aiki gadan-gadan kafin ƙarshen gwamnatin Muhammadu Buhari.

Da yake amsa tambaya kan takamaimen lokacin da Nigeria Air zai soma aiki, ministan ya ce “kafin ƙarshen wannan gwamnati, kafin 29 ga watan Mayu.”

Ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya za ta bar ɓangaren sufuri cikin yanayi mai kyau fiye da yadda ta tarar da shi kasancewar an cimma fiye da kashi 90 cikin 100 na taswirar da aka tsara cimma a ɓangaren.

legitnew

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp