Jakadan Turkiyya a Najeriya Hidayet Bayraktar ya ce, jiragen helikwafta da marasa matuƙi da ƙasarsa ke ƙerawa za su isa Najeriyar nan ba da jimawa ba da zimmar tallafa wa ƙasar wajen yaƙi da matsalar tsaro.
Kamfanin dillancin labarai na NAN, ya ambato Bayraktar na magana yayin bikin Ranar Tarayyar Turkiyya karo na 99 da aka gudanar a ofishin jakadancin ƙasar da ke Abuja ranar Asabar.
Ya bayyana yunƙurin a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar da ƙasashen suka ƙulla a 2021, yana mai cewa Turkiyya za ta faɗaɗa taimakon da take bai wa Najeriya wajen yaƙi da barazanar tsaro.
“Yarjejeniyar da ƙasashenmu suka saka wa hannu a shekarar da ta gabata abu ne na tarihi,” a cewarsa.
“Ina mai farin cikin sanar da ku cewa nau’i biyu daga cikin jiragen yaƙinmu irinsu na farko, maras matuƙi na Bayraktar (TB-2) da helikwafta (T-149) ATAK na gab da isowa Najeriya.
“Muna da ƙwarin gwiwa cewa sabbin kayan yaƙi na Turkiyya za su taimaka wa gwamnatin Najeriya wajen samar da zaman lafiya da kare dukiyar ‘yan ƙasa.”