Jirgin farko ɗauke da hatsi daga Ukraine zuwa Afirka tun bayan soma rikicin Rasha da Ukraine ya isa tashar ruwan Bahar Maliya ta Djibouti.
Jirgin ƙirar MV Brave Commander na dauke da ton 23,000 na alkama zuwa Ethiopia. An shafe mako biyu kafin isowa nan daga Bahar Aswad.
Ba kasafai ƴan jarida ke samun damar zuwa tashar jirgin ruwan da ke Djibouti ba amma mun zo nan saboda muhimmancin da isar kayan ke da shi.
Ƙaramar ƙasa ce mai yawan al’umma 900,000 amma tana da ɗaya daga cikin tashoshin ruwa mafi hada-hada a nahiyar.
Zai ɗauki kimanin mako guda kafin a ɗauki alkamar a kai Ethiopia mai maƙwabtaka kamar yadda hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya ta sanar.
Ethiopia na fuskantar mummunan fari cikin shekara 40 da kuma tashin hankali. In ji BBC.


