Wani jirgin sama mallakin kamfanin Delta Airlines na Amurka ya yi hatsari tare da kifewa a filin jirgi na Toronto a kasar Canada.
Hotunan da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda dusar ƙanƙara ta rufe jirgin.
Wakilin BBC ya ce wata sanarwa da kamfanin jirgin ya fitar ta ce dukkan fasinjoji 80 da ke cikin jirgin sun tsira, yayin da mutum uku – ciki har da ƙaramin yaro – ke tsananin jin jiki.