Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta tabbatar da cewa, jirgin farko na maniyyatan jihar zai tashi zuwa kasar Saudiyya, domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2023 a ranar Asabar 27 ga watan Mayu.
Sakataren zartarwa na hukumar Alhaji Umar Labbo ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Dutse ranar Lahadi.
Ya ce ana sa ran fara jigilar maniyyata na farko da mahajjata 395 daga filin jirgin saman Dutse na kamfanin Azman Air.
Labbo ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu hukumar ta yi aikin biza ga mahajjata sama da 1,500 tare da raba kayyaki da sauran kayayyaki ga maniyyatan aikin Hajjin bana.
Ya kara da cewa hukumar ta biya NAHCON kimanin Naira biliyan 4, wanda ya nuna kashi 100 na kudin aikin Hajjin 2023 na jihar.
A cewarsa: “Mun kammala dukkan shirye-shirye tare da masu ruwa da tsaki, ciki har da hukumomin tsaro, don samun nasara kuma ba tare da cikas ba.”