Kashin farko na ɗaliban da gwamnatin Kano ta ɗauki nauyin karatunsu a kasashen waje sun tashi daga filin jirgin sama na Mallam Aminu zuwa kasar Indiya.
Ɗalibai 150 ne mata da maza, wadanda gwamnatin Kano ta zaba zuwa karatun digiri na biyu a karkashin shirin gwamnatin na tura hazikan dalibai zuwa kasashen waje don zurfafa ilmi.
Rukunin na cikin dalibai 1,001 da ke da digiri mai daraja ta ɗaya da aka tantance kuma aka amince da tafiyarsu.


