Rundunar sojin Isra’ila ta ce jirgin farko dauke da ƙarin makaman Amurka ya isa sansanin sojin Isra’ila.
Shugaba Biden ya sha nanata cewa Washington za ta aika da karin harsasai da makamai masu linzami don taimakawa Isra’ila wajen yakar Hamas.
A cikin jawabinsa na baya-bayan nan, shugaba Biden ya bayyana hare-haren da kungiyar Hamas ta kai a karshen makon da ya gabata a Isra’ila a matsayin ayyukan ta’addanci.
Ya ce “Hamas, kungiya ce da babbar manufar kasantuwarta shine kashe Yahudawa, wannan ba karamin mugun aiki bane, sun yi wa ‘yan Isra’ila fiye da dubu daya kisan gilla, ciki har da Amurkawa 14.”
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai je kasashen Jordan da Isra’ila ranar Laraba domin tattaunawa kan matakan karfafa tsaron Isra’ila.