Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ba da rahoton cewa Faransa ta fara janye sojojinta daga Nijar, bisa umarnin gwamnatin mulkin soja.
An ambato kakakin babban hafsan hafsoshin Faransa na cewa “dakaru na farko sun fice.” daga kasar.
Tun da farko, shugabannin mulkin sojan Nijar sun ce dakarun Faransa za su fara fita daga kasar ranar Talatar nan cikin rakiyar sojojin Nijar.
Tun a watan Yuli ne aka fara zaman dar-dar tsakanin kasashen biyu, bayan juyin mulkin da ya hambarar da shugaban kasar Mohamed Bazoum.
Kimanin sojojin Faransa 1,500 ne ke taimakawa wajen yaƙi da masu iƙirarin jihadi a Sahel