Alamu na nuni da cewa gazawar da kamfanin jiragen sama na Emirates ya yi na maido da asusun sayar da tikitin da ya makale a Najeriya zuwa kasarsa ta Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) na iya sa kamfanin ya yanke shawarar dakatar da dukkan zirga-zirgar jiragen sama a ciki da wajen kasar.
Kamfanin jirgin a wata sanarwa da ya fitar a safiyar ranar Alhamis ya ce, zai dakatar da zirga-zirga daga Najeriya daga ranar 1 ga Satumba, 2022.
Akalla, dala miliyan 600 daga cikin kamfanonin jirage sama da 20 na kasashen waje an toshe a Najeriya tun farkon wannan shekara.
Kamfanin Emirates ya ce, kimanin makonni biyu da suka gabata a cikin wadannan kudade, tana da kusan dala miliyan 85 a Najeriya.
A ranar Litinin din da ta gabata ne kamfanin jirgin ya yanke mitoci 11 da yake yi a filin jirgin saman Legas zuwa bakwai kawai.
Wata sanarwa da mai ba da shawara kan harkokin yada labarai ga kamfanin jiragen sama a Najeriya ya fitar, ta yi zargin cewa duk kokarin da aka yi na dawo da kudaden ya ci tura, don haka ne ya sa aka dauki matakin dakatar da dukkan zirga-zirgar jiragen sama a kasar.


