Kamfanin sufurin jiragen sama na Emirates ya bayyana cewa zai koma zirga-zirga tsakanin Dubai ta Legas a Najeriya, shekara biyu bayan dakatar da jigilarsa a ƙasar.
Cikin wata sanarwa da kamfanin mallakin ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya fitar, ya ce zai fara jigilar fasinja tsakanin ƙasashen biyu sau ɗaya a kowace rana daga ranar 1 ga watan Oktoba.
“Jigila tsakanin Legas-Dubai ya kasance mafi shahara tsakanin kwastomominmu na Najeriya, don haka muna fatan dawo da wannan jigila domin kyautata wa kwastomominmu don inganta harkokin kasuwancinsu da tafiye-tafiyensu”, in ji mataimakin shugaban kamfanin Emirates Adnan Kazim.
A watan Satumban 2022, kamfanin ya dakatar da jigila zuwa Najeriya, sakamakon tangarɗa da ta shiga tsakanin kamfanin da gwamnatin ƙasar, kan mayar wa kamfanin kuɗinsa da ya kai kimanin dala miliyan 85.
Najeriya – wadda ta fi kowace ƙasa yawan al’umma a nahiyar Afirka – na fama da ƙarancin kuɗin waje, lamarin da ya tilasta wa ƙasar taƙaita kuɗaɗen wajen ƙasar da take bai wa masu zuba jari a ƙasar don kwashe ribarsu.
A watan Maris ne Babban Bankin Ƙasar, CBN ya ce ya warware duka basukan waje da ake bin ƙasar da ya kai dala biliyan bakwai.