An rufe ɗaya daga cikin titunan jirgin na filin jirgin sama na Abuja bayan wani jirgin fasinja mallakin Aerocontractors Airlines ya yi saukar gaggawa ranar Lahadi da safe.
Rahotonni sun ce lamarin ya faru ne da jirgi samfurin Boeing 737 mai rajista 5N-BYQ.
Sai dai an ci gaba da ayyuka kamar yadda aka saba ‘yan awanni bayan janye jirgin da ya maƙale.
Jirgin wanda ya taso daga Legas, ya yi yunƙurin sauka daga kan titin A4 ne lokacin da tayarsa ta gaba ta maƙale a cikin ciyayin da ke gefen titin.
“Daga baya an rufe titin har sai da aka janye jirgin,” in ji hukumar kula da lafiyar jirage ta Najeriya cikin wata sanarwa, tana mai cewa an ƙaddamar da bincike.
“Babu wanda ya rasa rai ko jin rauni,” a cewar James Odaudu cikin sanarwar.