Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta ƙasa, NRC, ta ce, ta kammala gyaran hanyar dogo daga Abuja zuwa Kaduna kwanaki 37 bayan da wasu ‘yan ta’adda suka kai masa hari.
Ta ce, za a ci gaba da zirga-zirgar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna nan ba da dadewa ba, tare da sanya karin matakan tsaro.
Hukumar ta NRC ta ce, lokacin da jiragen kasan suka koma, za a bukaci fasinjoji da su ba da rajistar lambar shaidar kasa (NIN), don tantancewa kafin su sayi tikitin jirgin kasa.
NRC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis ta hannun Engr Niyi Ali a madadin Manajan Darakta na kamfanin, Fidet Okhiria.
A ranar 28 ga watan Maris ne ‘yan ta’adda suka kai hari kan jirgin AK9 daga Abuja zuwa Kaduna, inda suka kashe akalla mutane tara tare da jikkata wasu da dama tare da yin awon gaba da wasu da dama.