Wani jirgi mai saukar ungulu da kamfanin mai na NNPCL ya ɗauka haya ya yi ɓatan dabo a safiyar ranar Alhamis.
Wata sanarwa daga kamfanin na NNPCL ta ce jirgin wanda ya tashi daga hedikwatar sojojin sama ta birnin Fatakwal, zuwa Nuims Antan wani wurin lodin mai da ke tsakiyar ruwa ya ɓace wa na’urar sadarwa da jirage da misalin ƙarfe 11:22 na safiyar ranar.
Sanarwar ta ce akwai mutum takwas a cikin jirgin.
Tuni ma’aikatan aikin ceto suka fara neman jirgin kuma kawo yanzu an gano gawar mutum uku.