Mutum huɗu sun mutu bayan hatsarin wani jirgin ɗaukar marasa lafiya mai saukar ungulu kudu maso yammcin Turkiyya.
Ma’aikata lafiyar ƙasar ta ce jirgin ya tashi ne daga asibitin horaswa da bincike, inda kuma ya ci karo da wani gini kafin ya faɗo ƙasa.
Ba a samu rahoton rasa rai daga cikin ginin da jirgin ya yi karo da shi ba.
Tuni dai aka ƙaddamar da bincike domin gano musabbain faruwar hatsarin jirgin, wanda rahotonni suka ce ya tashi a tsakiyar hazo. In ji BBC.