fidelitybank

Jiragen Najeriya mara sa matuƙa na daga da zuwa – Turkiyya

Date:

Jakadan Turkiyya a Najeriya Hidayet Bayraktar ya ce jiragen helikwafta da marasa matuƙi da ƙasarsa ke ƙerawa za su isa Najeriyar nan ba da jimawa ba da zimmar tallafa wa ƙasar wajen yaƙi da matsalar tsaro.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ambato, Bayraktar na magana yayin bikin Ranar Tarayyar Turkiyya karo na 99 da aka gudanar a ofishin jakadancin ƙasar da ke Abuja ranar Asabar.

Ya bayyana yunƙurin a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar da ƙasashen suka ƙulla a 2021, yana mai cewa Turkiyya za ta faɗaɗa taimakon da take bai wa Najeriya wajen yaƙi da barazanar tsaro.

“Yarjejeniyar da ƙasashenmu suka saka wa hannu a shekarar da ta gabata abu ne na tarihi,” a cewarsa.

“Ina mai farin cikin sanar da ku cewa nau’i biyu daga cikin jiragen yaƙinmu irinsu na farko, maras matuƙi na Bayraktar (TB-2) da helikwafta (T-149) ATAK na gab da isowa Najeriya.

“Muna da ƙwarin gwiwa cewa sabbin kayan yaƙi na Turkiyya za su taimaka wa gwamnatin Najeriya wajen samar da zaman lafiya da kare dukiyar ‘yan ƙasa.”

nnn.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp