Jiragen yaƙin Isra’ila “kusan 100” ne suka yi wa Zirin Gaza ruwan wuta a tsakar daren da ya gabata, a cewar Hafsan Sojin Sama na Isra’ila Birgediya Gilad Keinan.
Cikin wani saƙo a dandalin X, dakarun Isra’ila sun ce muradin sojin sama shi ne “lalata duk wani abu da ya shafi Hamas”.
Har yanzu ba a san adadin mutanen da hare-haren suka kashe ko jikkata ba, yayin da Isra’ila ta katse layukan sadarwa da kuma intanet a zirin.