Sakataren zartarwa na hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, Alhaji Mohammad Abba Danbatta, ya danganta tafiyar hajjin da alhazan kano ke yi zuwa kasar Saudiyya da gazawar jirgin da NAHCON ta ware domin jigilar maniyyatan.
Alhaji Mohammad Abba Danbatta wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin a Kano, ya ce kafin a fara jigilar maniyyatan zuwa kasar Saudiyya, hukumar ta rubutawa hukumar NAHCON a hukumance tana neman amincewar ta na baiwa kamfanin Max Air damar daukaka alhazai.
A cewarsa, “A jiya Azman ya umurce mu da mu kira alhazanmu, don jigilar kaya zuwa Saudiyya, mun gayyaci alhazai sama da 400, domin tantancewa a sansanin, kuma an bar maniyyatan a makale sama da sa’o’i 24.
Sakataren zartaswar ya ce, tun da aka fara aikin hajjin, Azman ya yi jigilar maniyyata 975 ne kawai.
Sai dai ya bayyana cewa, hukumar ta bukaci hakan ne saboda max air ya yi irin wannan atisayen tsawon shekaru da dama ba tare da wata tsangwama ba.
Mohammad Abba Danbatta ya lura cewa, duk da bukatar da NAHCON ta yi a hukumance ta baiwa kamfanin Azman Air da ya dauki nauyin alhazan Kano sama da dubu biyu.