Hukumar zaɓen mai zaman kanta ta INEC ta ce, ci gaba da jinkiri wajen amincewa da dokar zabe na shekarar 2010 da Majalisar Dokokin ƙasar nan ta yi na iya yin tasiri kan amincewa da sabbin gyare-gyare a babban zaben 2023.
Hukumar ta ce, duk da cewa ta na gudanar da ayyukanta ne bisa tsarin dokokin da ake da su, amma ya na da muhimmanci a samar da dokar da za ta jagoranci gudanar da zaben akalla watanni 12 zuwa 18 kafin gudanar da zaben.
Tuni dai shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu, ya bayyana cewa a ranar 23 ga watan Fabrairun 2023 a matsayin ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa, wato nan da shekara daya kenan.
Gyaran dokar zaben dai ya haifar da muhawara a Najeriya, musamman kan bukatar yada sakamakon zaben ta shafin Internet, da kuma zaɓen .yar tinƙe ga kowacce jam’iyya.