fidelitybank

Jikar Nelson Mandela ta mutu

Date:

Zoleka Mandela, jikar zababben shugaban kasar Afirka ta Kudu na farko ƙarƙashin dimokuradiyya, Nelson Mandela, ta rasu tana da shekaru 43 sakamakon kamuwa da cutar daji.

Iyalanta sun sanar da rasuwar ta a shafin Instagram, inda suka bayyana cewa ‘yan uwa da abokan arziƙi da dama sun kewaye gawar tata.

A cikin ‘yan shekarun nan ta shahara wajen bayar da bayani game da cutar dajin da take fama da ita da kuma bayyana tarihinta na ɗabi’ar shan ƙwayoyi da tsananin damuwar da take shiga da kuma yadda aka yi lalata da ita tun tana ƙarama.

Zoleka ta kuma yi kamfe don samar da ingantaccen tsaro a kan titi bayan mutuwar diyarta mai shekaru 13 a wani hatsarin mota a shekarar 2010. Zoleka ta rubuta tarihin rayuwarta, wanda ta yi wa laƙabi da ‘when hope whispers’.

Ta kuma yi fama da cutar kansar nono sama da shekaru goma da suka wuce.

A shekarar da ta gabata ne ta tabbatar da cewa tana da cutar daji a hanta da huhu, daga nan kuma ta yadu zuwa wasu sassan jikinta.

the nation newspaper 
today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp