Jikan Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, Alhaji Hassan Danbaba,ya rasu a Kaduna ya na da shekaru 51.
Danbaba, wanda shine shugaban masu nadin sarki a masarautar Sokoto ya yanke jiki ya fadi ne da rana a cewar rahotanni.
Kimanin shekara guda bayan rasuwar mahaifiyarsa, Aishatu, babban yar marigayi Firimiyan na Sokoto, Sir Ahmadu Bello.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, wani majiya na kusa da iyalansa, Alhaji Buhari Sarkin Tudun Jabo, ya tabbatar da rasuwar Danbaba a jihar Kaduna, bayan gajeriyar rashin lafiya.