Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya Nimet, ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu yankunan ƙasar nan.
Nimet ta kuma gargaɗi mazauna wasu yankunan jihohin arewacin ƙasar tara su zama cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon yiwuwar samun ambaliya.
Jihohin da ake sa ran samun ambaliyar sun haɗa da Jigawa da Yobe da Gombe da Plateau da Bauchi da Nasarawa da Kaduna da Katsina da kuma Kano.
Hukumar ta buƙaci mazauna kwari da waɗanda ke zaune a kusa da koguna a waɗannan jihohi su ɗauki mataki tare da zama cikin shiri.