fidelitybank

Jihohin da APC da PDP suka samu gwamna

Date:

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta samu nasarar cinye kujerun gwamna 15 a sakamakon da aka bayyana kawo yanzu a zaɓen ranar Asabar 18 ga wata da aka gudanar a faɗin jihohin ƙasar 28.

Yayin da jam’iyyar PDP mai hamayya ta samu kujerun gwamna takwas, sai kuma Jam’iyyar NNPP wadda ta samu kujerar gwamna ɗaya.

Jam’iyyar APC ta samu nasara a jihohin Sokoto da Katsina da Jigawa da Gombe da Lagos da Kwara da Niger da Yobe da Nasarawa da Cross Rivers da Ebonyi da Ogun da Benue da Kaduna da kuma jihar Borno.

Sai kuma jam’iyyar PDP da ta samu nasara a jihohin Plateau da Bauchi da Oyo da Delta da Rivers da Akwa Ibom da Zamfara da kuma jihar Taraba.

Sai jam’iyyar NNPP da ta samu nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar Kano.

Haka kuma hukumar zaɓen ta dakarar karɓar sakamakon jihohin Abia da Enugu, saboda rashin jituwa da aka samu tsakanin wakilan jam’iyyu a wasu ƙananan hukumomi.

Sannan kuma hukumar ta INEC ta ayyana sakamakon jihohin Kebbi da Adamawa a matsayin wanda bai kammala ba.

Gwamnoni a Najeriya dai na da tasiri tare da ƙarfin faɗa-a-ji a siyasar ƙasar, inda suke juya kasafin kuɗin jihohinsu.

the sun newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp