Ƙungiyar ƴan fansho na arewacin Najeriya, NUP ta ce jihohi huɗu cikin 19 na arewacin Najeriya ne kaɗai suke biyan mafi ƙarancin fanshon naira 32,000 da gwamnatin tarayya ta tsara.
Da yake bayani a taron shiyya na ƙungiyar a Kaduna, shugaban ƙungiyar, Kwamrade Mohammed Sali ya bayyana lamarin da “rashin adalci” da ya ce ake yi wa tsofaffin ma’aikatan bayan sadaukar da rayuwarsu da suka yi wajen aikin al’umma, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
“Jihohi huɗu ne kacal ke biyan mafi ƙarancin fansho na naira 32,000 a arewacin Najeriya mai jihohi 19. Akwai jihohin da suke biyan fanshon naira dubu 3,000 da 4,000 da 5,000,” in ji shi, inda ya ƙara da cewa ƙungiyar za ta fi mayar da hankali kan neman hanyoyin sasanci maimakon fito na fito da gwamnatocin jihohin.
“Ba za mu yi fito na fito da gwamnonin jihohin ba domin mu iyaye ne. Kuna so ku ga iyayenku a tituna suna gudanar da zanga-zanga? za mu zagaya jihohin mu tattauna da hukumomi domin samun sasanci cikin lumana,” in ji Sali.