Hukumar alhazai ta ƙasa NAHCON, ta yi kira ga jihohi da su hanzarta biyan wani ɓangare na kuɗaɗen hajjin maniyatan jihohinsu kafin watan Disamban bana domin tabbatar da kujerun da aka keɓe musu.
A wata wasika da aka aika wa shugabannin hukumoin alhazai na jihohi, darektan harkar kudi na hukumar, Dr Salihu Usman ya bayyana cewa kiran ya zame dole bisa la’akari da wa’adin biyan kuɗi da ma’aikatar hajji ta saudiyya ta bayar.
A cewarsa rashin biyan kudaden kafin cikar wa’adin zai sanya hukumar ta ɗauki matakin rage yawan kujerun da aka bai wa jihohin.
NAHCON ta yi kira ga hukumonin jihohin da su bayar da cikakken goyon baya don tabbatar da nasarar aikin Hajjin 2024.


