Jihohi shida na tarayya sun maka gwamnatin tarayya a gaban kotun koli suna neman a soke zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 da ya gabata.
Jihohin shida da suka shigar da karar ta hannun babban Lauyan su sun hada da Adamawa, Akwa Ibom, Bayelsa, Delta, Edo da Sokoto.
An shigar da karar ne bisa ga sashe na 6 (6)14(3)153(2) da 252 na kundin tsarin mulkin kasar na 1999 da kuma hurumin kotun kolin.
Suna rokon kotun koli ta yi amfani da wasu tanadin doka don soke zaben bisa zargin tafka magudi da rashin adalci.
Jihohin dai na son kotun kolin ta bayyana cewa kotun ta soke shelar dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Ahmed Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Suna neman “Sanarwa cewa daukacin sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 da shugaban INEC ya sanar a cibiyar tattara bayanai ta kasa, Abuja, wanda ya sabawa tanadin sashe na 25; 47 (2); 60 (1), (2), (4) & (5); 62; 64 (4) (a) & (b); 70; da kuma 148 na dokar zabe, 2022, da ke gudanar da zabukan 2023 a fadin kasar, musamman sakin layi na 38 na dokokin INEC da ka’idojin gudanar da zabe, 2022; da sakin layi na 2.8.4; 2.9.0; da 2.9.1 na kundin tsarin zabe na INEC na shekarar 2023, don gudanar da zaben shugaban kasa, ba shi da inganci, ba shi da amfani, kuma ba shi da wani tasiri.