fidelitybank

Jihar Oyo har yanzu ba ta karbi kudin da Tinubu ya ce ya baiwa jihohi – Gwamna

Date:

Gwamanan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya musanta maganar da Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya yi cewa gwamnatin tarayyar ƙasar ta bai wa jihohi, sama da naira biliyan 570, domin tallafa wa jama’a

A jawabinsa na neman kwantar da hankalin al’ummar ƙasar da ke zanga-zangar tsadar rayuwa da rashin shugabanci na gari, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta raba kuɗin ga gwamnonin jihohin ƙasar 36 na ƙasar, domin sauƙaƙa wa jama’a matsin rayuwa.

Ƙari a kan waɗannan kuɗaden Shugaba Tinubu ya ce, gwamnatin tasa, ta kuma bai wa ƙananan harkokin kasuwanci 600,000 tallafi, sannan kuma akwai wasu ƙarin ƙananan sana’o’in 400,000 da za su amfana da tallafin su ma.

To amma Gwamnan na jihar Oyo, Seyi Makinde a wani saƙo da ya sanya a shafinsa na X,a jiya Alhamis, ya ce shi dai jiharsa ba ta san da wannan kuɗi da Tinubun ya ce gwamnatinsa ta raba wa jihohi ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan ya ce yana mayar da martani ne kan maganar da wani ɗan jihar tasa ya yi kan iƙirarin gwamnatin tarayyar cewa ta bai wa jihohi sama da naira biliyan 570 domin tallafa wa jama’a kan ƙuncin rayuwa.

Mista Makinde ya ce, maganar na daga irin babtutuwan da gwamnatin tarayyar ke yi ne na faɗin abin da ba haka yake ba, yana mai ƙarin bayani da cewa : ” Kuɗaden da ake magana na daga cikin rancen bankin duniya na shirin NG-CARES, wanda kuɗi ne da ake tallafa wa jihohi wajen farfaɗowa daga annobar Korona, inda jiha za ta yi amfani da kuɗinta ta aiwatar da shirin, daga baya kuma bankin duniya ya mayar mata da kuɗin ta hanyar gwamnatin tarayya bayan bankin ya tantance abubuwan da jihar ta yi da nasarorin da ta samu.

Ya ce, ” Ya kamata ma fa a sani cewa kuɗin na bankin duniya bashi ne ga jihohi ba tallafi ba, saboda haka jihohi za su biya kuɗin.

Gwamnan ya ce jiharsa, Oyo, ta samu kuɗin ne, kashi biyu, inda a kashin farko aka ba ta naira biliyan 5.98, sannan a kashi na biyu ta samu naira biliyan 822.

”Saboda haka a taƙaice gwamnatin tarayya ba ta ba jihar Oyo wani kuɗi ba.

Makinde shi ne gwamnan jam’iyyar PDP, na biyu da ya soki Tinubu a kan jawabin a kwanakin nan.

Na farko shi ne Gwamna Bala Mohammed na Bauchi da ya ce jawabin shugaban soki-burutsu ne kawai – ko holoƙo ne – hadarin kaka.

legit news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...
X whatsapp