Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta sanar da cewa sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar, Faleye Sunday Olaleye, da aka tura wa hukumar ya fara aiki.
A wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Yemisi Opalola, ya ce, zuwan sabon Kwamishinan ya biyo bayan karin girma da aka yi wa tsohon kwamishinan ‘yan sanda, AIG Olawale Olokode.
A cewar sanarwar, an haifi sabon kwamishinan ‘yan sandan, Olaleye a garin Iyin-Ekiti, karamar hukumar Ifelodun/Irepodun ta jihar Ekiti.
“Kwamishanan ‘Yan Sanda, wanda ke rike da M.SC a fannin Gudanar da Jama’a da B.SC a fannin Geography. An nada shi aikin ‘yan sandan Najeriya a watan Maris, 1990 a matsayin Cadet Assistant Superintendent of Police (Cadet ASP).
“CP Faleye Olaleye, ya yi aiki a Jihohin kasar da dama. Wasu daga cikin Jihohin da ya yi aiki sun hada da: Delta, Ekiti, Oyo, Ondo, Osun, Ebonyi, Plateau, Taraba, FHQ Abuja/Lagos, Zone 5 Benin, Zone XI Osogbo, Angola (United Nations) tsakanin wasu.