fidelitybank

Jihar Edo ta rage kwanaki biyu a mako ga dalibai a kan tsadar fetur

Date:

Gwamnatin Jihar Edo, ta mayar da ranakun zuwa makaranta sau uku a sati da zimmar rage raɗaɗin cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi.

Shugabar hukumar ilimin bai-ɗaya ta Edo State Universal Basic Education Board (SUBEB), Ozavize Salami ce ta bayyana hakan a Birnin Benin ranar Juma’a, kamar yadda kafar Channels TV ta ruwaito.

An ɗauki matakin ne bayan ganawar da ta yi da sauran hukumomin gwamnatin jihar domin fara aiki da umarnin gwamnati na rage yawan ranakun aiki daga biyar zuwa uku a makon da ya gabata.

“Game da matakin rage ranakun aiki zuwa uku a sati, mun yi ƙoƙarin mayar da ranakun zuwa makaranta cikin kwana ukun farko na kowane mako,” in ji ta.

Ta ƙara da cewa: “Ba ma son a samu wani tazgaro game da tsarin tafiyarwa. Saboda haka yara za su je makaranta a ranakun Litinin, da Talata, da kuma Laraba a dukkan makarantun firamare.

“Abin da muka yi shi ne, mun tsawaita lokacin koyarwa da awa ɗaya a firamare da kuma awa biyu a sakandare don tabbatar da cewa an cimma manhajar karatu da aka tsara.”

legit nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...

Isra’ila ta buga gangar yaƙi – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce...

Iran ta na cigaba da luguden makami mai Linzami cikin Isra’ila

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Isra'ila yayin...

Alhazan Najeriya sun fara dawo wa daga ƙasar Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da isowar...

Sojoji sun kama ɗan kasar China da zargin kai wa ƴan Boko Haram kayayyaki

Rundunar sojojin ƙasar nan ta kama wani dan kasar...

Isra’ila ta tsokano tsuliyar Dodo – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce...

Da sani na Isra’ila ta kai hari Iran – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana sane...

Farashin man fetur ya tashi bayan Isra’ila ta kai wa Iran hari

Farashin man fetur a kasuwannin duniya ya tashi bayan...

Isra’ila ta kashe manyan Jami’an tsaron Iran su biyar

Wani hari da Isra'ila ta kira ‘Operation Rising Lion’,...

Isra’ila ta kashe Manyan Jami’an Iran biyar a hare-hare

Wani hari da Isra'ila ta kira ‘Operation Rising Lion’,...
X whatsapp