fidelitybank

Jiha ta uku a Amurka ta amince a rinka mayar da Gawa zuwa kasa

Date:

Jihar New York ta zama jihar Amurka ta baya-bayan nan da za ta bayar da dama a rinƙa mayar da gawarwaki ƙasa.

Hakan na nufin mutum zai iya bayar da umarni a mayar da gawarsa ƙasa idan ya rasu – wanda wasu ke ganin hakan yana da kyau ga muhalli maimakon a binne mutum ko kuma a ƙona gawarsa.

Idan za a yi hakan, akan saka gawar mutum ne a cikin wani akwati a rufe shi tsawon makonni domin gawar ta ruɓe bayan an gauraya ta da wasu abubuwan da za su taimaka ta zama ƙasa.

A 2019, Washington ta zama jihar Amurka ta farko da ta halasta wannan lamari. Sai kuma daga baya Colarado da Oregin da Vermont da California suka biyo baya. Hakan na nufin New York ta zama jiha ta shida a Amurka da a hukumance ta amince da hakan bayan gwamnan New York, Kathy Hochul a ranar Asabar ya saka wa dokar hannu.

Ana saka gawar a cikin wani ɗan dogon ƙwarya-ƙwaryan sunduƙi sa’annan ana jefa wasu abubuwa a ciki kamar irin su dusar katako da da ciyawa da wasu furanni inda a hankali gawar take ruɓewa ta gauraye da suaran abubuwan da ke haɗe da gawar.

Bayan kimanin wata guda – da kuma ɗumama gawar domin kashe duk wani abu da zai iya zama ƙwayar cuta, ana ɗaukar ƙasar da gawar ta zama domin bai wa iyalan mamacin . Za a iya amfani da ƙasar wadda ta samo asali daga gawa domin shuka bishiyoyi ko furanni ko kayan lambu.

Wani kamfanin Amurka mai suna Recompose ya ce aikin da yake yi zai iya rage sinadarin carbon mai ɗunbin yawa idan aka kwatanta da ƙona gawa. Fitar da sinadarin carbon na daga cikin abubuwan da suke jawo sauyin yanayi sakamakon suna ɗaure yanayin zafin da duniya ke da shi.

Haka kuma binne mutum a cikin akwatin gawa wanda ake yin sa da katako shi ma yana jawo asarar katako da kuma ainahin filin da ake rufe mutum da sauran albarkatun ƙasa.

Kamfanin ya ce matakin mayar da gawar mutum ƙasa yana da amfani matuƙa ba wai don kiyaye muhalli kawai ba, amma don samun sauƙi a biranen da ake ƙarancin maƙabartu domin binne mutane.

besda salary

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp