Daya daga cikin jiga-jigan masarautar Katsina, Alhaji Nuhu Abdulkadir ya rasu.
Rahotanni sun ce, Hakimin Kauran Katsina, kuma Hakimin Rimi mai shekaru 77 ya rasu ne a gidansa da sanyin safiyar ranar Talata.
Ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya jim kadan bayan ya yi bikin cika shekaru 40 a kan karagar mulkin Rimi.
Wani dan uwa mai suna Alhaji Aminu Nuhu-Abdulkadir ya tabbatar da rasuwarsa.
Za a yi jana’izar marigayin da rana kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Ana ci gaba da shirye-shiryen jana’izar.
Kafin rasuwarsa, an zarge shi da zargin sace Habiba Isyaku ‘yar shekara 17 da kuma auren dole.


