Tsohon Kwamishinan Muhalli na Jihar Enugu, Cif Chijioke Edeoga, ya zama dan takarar gwamna a jam’iyyar Labour a jihar.
Edeoga, wanda ya kafa jam’iyyar PDP a jihar, ya yi takara a zaben fidda gwani na gwamna a jam’iyyar amma Peter Mbah ya sha kaye a yayin atisayen.
An yi ta rade-radin cewa, Edeoga ya koma jam’iyyar Labour ne kuma ya karbi tikitin takarar gwamna a yammacin ranar Asabar.
Shi ma wani Shugaban jam’iyyar na jihar Enugu ya yi tsokaci cewa, tsohon kwamishinan ya fice daga jam’iyyar PDP ya samu tikitin jam’iyyar Labour Party.
Edeoga, a wata tattaunawa ta wayar tarho da safiyar Lahadi, ya tabbatar da hakan, yana mai cewa, “eh, gaskiya ne. Yanzu ni ne dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour.”