Alhaji Ibrahim Gidado, mai ba Gwamna Aminu Tambuwal shawara na musamman na jihar Sokoto, ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bashar Abubakar, mai taimaka wa Sanata Aliyu Wamakko (APC- Sokoto ta Arewa) kan harkokin yada labarai ya fitar ranar Lahadi a Sokoto.
Gidado wanda ke wakiltar mazabar Sokoto ta Kudu ya samu tarba a jam’iyyar APC a ranar Asabar da ta gabata ta hannun shugaban jam’iyyar na jihar Wamako.
Sanarwar ta ruwaito Gidado yana cewa, shi da magoya bayansa sun fice daga PDP ne bisa zargin rashin mayar da hankali da amincewa daga shugabanninta.
“Mun shiga jam’iyyar APC da shugabanninta ne, domin hada kai mu kwato jihar Sokoto daga gwamnatin Tambuwal da ta gaza, saboda alkawura da yawa da aka dauka ba a cika ba.”
Hakazalika, Wamakko ya bayyana farin cikinsa da karbar sabon dan jam’iyyar tare da ba shi tabbacin za a yi masa daidai wa daida. A cewar NAN.