Gwamnatin jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya za ta ƙulla hulɗar kasuwanci tsakaninta da wani kamfanin Saudiyya da ke noman dabino domin bunƙasa noman dabino a jihar.
Gwamnan jihar Umar Namadi ne ya bayyana haka a lokacin da ya karɓi baƙuncin ma’aikatan kamfani mafi girma a Saudiyya a fannin noman dabino da kula da aikin gona, karƙashin jagorancin Abdul’aziz Abdurrahman Al-Awf a Dutse, babban birnin jihar.
Abdul’aziz Al-Awf ya ce kamfaninsu za ta samar da tsarin noma na zamani domin ganin an yi noman dabino a tsawon shekara ba sai kaka ba, wanda za a cimma ta hanyar horar da manoma, karfafawa matasa da kuma amfani da wasu daga cikin ire-iren dabino na Saudiyya da ke samar da amfani mai yawa ta yadda jihar za ta zama kan gaba a noman dabino a Najeriya da Afrika.
Gwamnan jihar ya bayyana cikkakiyar goyon bayansa ga shirin, inda ya ce hakan ya yi dai-dai da manufarsa ta bunƙasa fannin noma.
Ya ce ko a yanzu ma jihar ce ta fi kowacce samar da dabino a Najeriya, kuma burinsu shi ne samar da adadin dabinon da ake buƙata a ƙasar har ma a fitar da shi ƙasashen waje.
Samfurin dabino na Mejdool (Meju) da Barhi (Bari) da Sukkari (Sukari) da kuma Ajwa ne aka bayyana a matsayin waɗanda suka dace a yi noman su a Jigawa.