Yayinda ake shirin zaben 2023, tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya ziyarci magabacinsa, Sanata Danjuma Goje, a gidansa dake birnin tarayya Abuja.
Dankwambo ya je gidan Goje tare da manyan jiga-jigan jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP irinsu Gwamnan jihar RIvers, Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose; da Sanata mai wakiltan Abuja, Sanata Philip Aduda.
Ziyarar wacce akayi a sirri a unguwar Asokoro, ana kyautata zaton na kokarin jan ra’ayin Goje ya koma jam’iyyar PDP, rahoton Leadership.