Shugaban kungiyar gwamnonin Kudancin kasar nan kuma gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, tare da sauran masu ruwa da tsaki, a ranar Litinin, sun gargadi jam’iyyar APC kan shirin tsayar da tikitin takarar shugaban kasa a 2023 zuwa Arewa.
Wasu jiga-jigan ‘yan kasar da suka yi magana kan wannan batun da suka hada da Sanata Ali Ndume da babban jigo a kungiyar Kwamared Frank Kokori, sun ce makircin ya zama barazana ga daidaiton kasar nan.
Hankulan jama’a ya biyo bayan sanarwar da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya yi na cewa jam’iyyar ba ta ware tikitin tsayawa takara a Kudu ba.
A ranakun 30 da 31 ga watan Mayu ne ake sa ran gudanar da babban taron shugaban kasa na jam’iyyar.