Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Attahiru Jega, ya caccaki Ministan Kwadago da Aiki, Chris Ngige, kan mayar da matakin masana’antu da kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta yi zuwa rikicin kashin kai.
Da yake magana a ranar Talata yayin wani shiri a gidan talabijin na Arise, Jega ya ce Ngige yana haifar da matsaloli fiye da mafita.
Gwamnatin tarayya ta yi gaba da yin rijistar kungiyoyin ma’aikatu a bangaren ilimi.
Kungiyoyin dai sun hada da kungiyar kwararrun likitoci da hakori ta kasa NAMDA da kuma Congress of Nigerian University Academics, CONUA.
“Abin takaici, a yanzu, ministan kwadago ba ya taimakawa al’amura. Ya mayar da wannan rikici tsakanin sa da ministan ilimi a daya bangaren kuma tsakaninsa da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) a daya bangaren,” in ji Jega.
“Yayin da wasu da dama ke kokarin lalubo hanyar magance wannan al’amari domin dalibai su koma makaranta su kuma ASUU su koma bakin aiki, ya shagaltu da samar da kalubale.
“Yanzu ya kai maganar gaban kotun masana’antu, a yau ya yi rajistar kungiyoyi biyu kuma yana kokarin haramta kungiyar ASUU.
“Idan wannan gwamnati ta yarda da hakan, ina ganin wannan wani girke-girke ne na bala’i kuma yana iya haifar da matsaloli fiye da yadda za a magance wannan batu na yajin aiki a jami’o’i.”
ASUU dai ta shiga yajin aikin ne tun a watan Fabrairun 2022 domin matsa lamba kan bukatar inganta kudade ga jami’o’in, da kuma duba albashin malaman jami’o’i da dai sauransu.