A karon farko a cikin watanni tara, Elon Musk ya tashi daga kasancewa mutumin da ya fi kowa kuɗi a duniya.
Jeff Bezos ya maye gurbin Musk, bayan hannayen jarinsa na kamfanin Tesla ya fadi da kashi 7 da digo biyu cikin ɗari a ranar litinin.
Maunin hamshaƙan masu kudi na Bloomberg ya nuna cewa a yanzu Musk yana da arzikin da yawansa ya kai dalar Amurka 197.7 billiyan, yayin da shi kuma Beros ke da dala 200.3 billiyan.
Haka kuma wannan ne karon farko da hamshaƙin mai kuɗin, mai shekara 60 a duniya, mai kamfanin Amazon ya ɗare wannan matsayi na hamshaƙan masu kuɗin duniya na Bloomberg tun shekarar 2021.
Giɓin duniya da ke tsakanin Musk, mai shekara 52 a duniya da kuma Bezos, wanda a baya ya kai dala $142 biliyan, yana raguwa yayin da hannayen jarin Tesla da Amazon ke yin hannun babbar riga.
Duk da cewa duka kamfanonin biyu na daga cikin waɗanda suka fi bunƙasa kasuwar shunku ta Amurka, sai dai hannayen jarin Amazon ya ruɓanya tun shekarar 2022 ya zamo mafi ƙarfi.
Yayin da na Tesla kuwa ke faɗuwa da kusan kashi 50 cikin ɗari tun bayan ganiyarsa a shekarar 2021.