fidelitybank

Jaurimin Bollywood Saif Ali Khan ya tsallake rijiya da baya yayin da aka caccaka masa wuka

Date:

An yi wa fitaccen jarumin fina-finan Bollywood ɗin nan, Saif Ali Khan tiyata kuma yana samun sauƙi bayan daɓa masa wuƙa a lakarsa da wani mutum ya yi bayan ya kutsa cikin gidan jarumin, kamar yadda masu taimaka masa suka ce.

Harin dai ya faru ne da safiyar ranar Alhamis a unguwar da jarumin da iyalansa ke zaune a wajen birnin Mumbai.

Ƴansanda sun shaida wa BBC cewa an dai kai wa jarumin harin ne sakamakon wata hatsaniya da ta ɓarke tsakaninsa da wani mutum da ba a san kowane ne ba wanda ya kutsa har cikin gidan jarumin da tsakiyar dare.

Zuwa yanzu ba a samu cikkaken bayani kan harin ba.

” Daga nan sai gardama ta ɓarke tsakanin Khan da maharin, ” kamar yadda mataimakin kwamishinan ƴan sandan Mumbai Dixit Gedam ya shaida wa BBC.

An garzaya da Khan asibitin Lilavati da ke birnin Mumbai da safiyar Alhamis.

Niraj Uttamani, wani babban jami’i a asibitin ya shaida wa BBC cewa an daɓawa khan wuƙa sau shida, amma biyu ciki sun fi muni.

Masu taimakawa Khan sun ce lamarin ‘ƙokarin yin sata ne” sai dai ba su bayyana wasu ƙarin bayanai ba.

” Mu na buƙatar ƴan jarida da magoya bayansa su yi haƙuri su kwantar da hankalinsu. Lamarin ya na hannun ƴan sanda,” a cewar su.

Ƴansandan dai sun haɗa wata tawagar da za ta binciki al’amarin.

“An yi wa Khan tiyata kuma ya fito lafiya. Yanzu haka yana murmurewa kuma likitoci na sa ido kansa,” a cewar masu taimakawa Khan cikin wata sanarwa.

Da yake magana da manema labarai bayan tiyatar, Dakta Nitin Dange na asibitin Lilavati inda aka kwantar da Khan, ya ce jarumin ya samu mummunan rauni a laƙarsa sakamakon daɓa masa wuƙa a lakar.

” An gudanar da tiyata domin cire wuƙar da kuma gyara tsiyayewar lakar. Tawagar masu tiyata sun kuma yi aikin gyara munanan ciwuka biyu da ke hannunsa na hagu da ɗaya a wuyansa, ” inji shi.

Khan na auren jarumar Bolloywood Kareena Kapoor kuma ma’auratan na da ƴaƴa biyu.

Zuwa yanzu ba a ji ta bakin iyalinsa ba, sai dai masu taimakawa Khan sun tabbatar da cewa suna cikin ƙoshin lafiya.

mmm.nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mun bayar da hutu ranar Litinin bisa jimamin mutuwar ƴan Wasa – Gwamnatin Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar...

Tun farko na shaida wa Tinubu ba zan zaɓe shi ba – Amaechi

Tsohon ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce...

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...

Sojoji sun ce sun hallaka ƴan Ta’adda 60 a jihar Borno

Dakarun sojijin Operation Haɗin-Kai sun ce sun kashe ƴan...

Zan cigaba da jajircewa a kan rantsuwar da na yi ta kujera ta – Fubara

Gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya...

Ambaliya ya kashe Mutane a jihar Neja

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun...

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamnan Edo

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta amince da...

An kashe aƙalla mutum 10,217 a mulkin Tinubu – Amnesty

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan...

Gwamnati ba ta tausayin Talaka – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben...

Elon Musk ya ajiye aikin da Trump ya naɗa shi

Hamshaƙin attajirin nan Elon Musk ya sanarda aniyarsa ta...
X whatsapp