fidelitybank

Jarumin Nollywood da ya yi wa Tinubu addu’a tsigidir ya fadi dalilansa

Date:

Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood kuma furodusa, Ebun Oloyede, wanda aka fi sani da Olaiya Igwe, ya bayyana dalilin da ya sa ya tafi tsirara a bakin teku domin yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) addu’a, Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara a zaben 2023.

Jarumin, a wani faifan bidiyo da aka watsa a shafin sa na Instagram ranar Asabar, an ga shi tsirara, yana addu’ar samun nasara ga Tinubu a bakin teku.

A cikin sakon nasa, Olaiya Igwe ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Legas shine “dan takara daya tilo da ke nuna kimarmu da kyawawan manufofinmu. Kuma shugaban da zai yi fafutuka wajen ganin ya cika alkawarin da Najeriya ta yi wa al’umma masu zuwa.”

Instagram ya goge asusunsa saboda keta dokokinsa na tsiraici da batsa.

Ku tuna cewa a baya jarumin ya bayyana Tinubu a matsayin wanda ya taimaka masa domin ceto rayuwarsa bayan an gano shi da ciwon nephrolithiasis (Kidney Stones) ba tare da saninsa ba.

Mabiyan Olaiya a shafukan sada zumunta sun nuna rarrabuwar kawuna kan yanayin da ya zabi nuna goyon bayan sa. Yayin da mutane da yawa suka yi imanin cewa zai iya bayyana kansa ta kowace hanya da yake so, wasu suna ganin ya kamata ya yi amfani da wasu ladabi.

nigeria legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp