Masana’antar fina-finan Najeriya na Nollywood, sun sake shiga cikin makoki sakamakon rasuwar Murphy Afolabi.
Shahararren dan wasan Yarbawa mai shekaru 49 ya rasu da sanyin safiyar yau a gidansa.
Fitaccen daraktan fina-finai kuma furodusa, Tunde Ola-Yusuf ya tabbatar da rasuwar ta shafinsa na Facebook a yammacin Lahadi.
“Ki huta lafiya. Allah ya baiwa iyalai da makusanta karfin gwiwar jure wannan rashi,” ya rubuta.
Marigayin ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa ne sama da mako guda da ya gabata, daidai ranar Juma’a 5 ga watan Mayu.
Murphy, wanda ya fara aikinsa da fim mai suna ‘Ifa Olokun’ karkashin jagorancin Dagunro, ya fito a ciki tare da samar da wasu da dama.