Fitaccen Jarumi da kuma mai shirya fina-finan Indiya, Manoj Kumar, ya mutu yana da shekara 87.
Jarumin ya mutu ne a birnin Mumbai bayan fama da jinya da ke da alaƙa da tsufa, a cewar DrSantosh Shetty na asibitin Kokilaben Dhirubhai Ambani, inda aka kwantar da shi.
Ɗan fitaccen jarumin, Kunal Goswami, ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na ANI cewa Kumar ya shafe tsawon lokaci yana fama da rashin lafiya.
Kumar dai ya bar gagarumin tarihi a masana’antar shirya-shirya fina-finai ta Indiya, inda ya haska a fina-finai da dama ciki har da Dus Numbari – waɗanda suka shi shahara a shekarun 1960 zuwa 1970.
Ƴan siyasa da taurari da kuma masoyansa na ta alhinin rasuwar tasa a shafukan sada zumunta.
Firaiminista Narendra Modi ya kira shi da “shahararren jarumi da ya haska sinimun Indiya”.
“Muna alfahari da ayyukan Manoj kuma za su ci gaba da ƙara wa masu tasowa ƙwarin gwiwa,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.