fidelitybank

Jarumin da ya fito a fina-finan Bollywood 250 ya mutu

Date:

Fitaccen jarumi kuma furodusa a masana’antar fina-finai ta Bollywood ta kasar Indiya, Ramesh Deo, ya mutu sakamakon bugun zuciya.

Dan jarumin ne ya sanar da mutuwarsa a daren ranar Laraba, inda ya ce, mahaifinsa ya mutu ne a ranar a asibitin Kokilaben Dhirubhai Ambani, ya na da shekara 93 a duniya.

Ramesh ya fito a fina-finan Indiya sama da 250, ya kuma shafe wajen shekara 60 a na damawa da shi a masana’antar Bollywood.

Jarumin ya yi fice wajen taka rawa daban-daban a cikin fina-finai, tun daga kan likita, mugu, mahaifi da sauransu.

Wasu daga cikin fina-finansa da suka yi fice sun hada da Aarti, Anand, Aap Ki Kasam, Mere Apne, Jeevan Mrityu, Saraswatichandra, Teen Bahuraniyan, Khilona, Ghayal Once Again, Jolly LLB da sauransu.

Kazalika, Ramesh ya ci gaba da fitowa a fina-finai masu dogon zango na yankin Marathi da sauran shirye-shiryen gidajen talabijin.

An haifi Ramesh Deo ne a yankin Amravati Maharashtra, sannan ya fara fitowa a fina-finai a 1951 a cikin fim din Paatlaachi Por.

Ramesh ya bar mata daya mai suna Seema Deo da kuma ’ya’ya biyu, Ajinkya Deo da kuma Abhinay Deo.

nigeria daily post

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp