Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi kira ga dukkan jam’iyyun siyasa a kasar da su ajiye batutuwan zabe a gefe guda, kuma su hada hannu da gwamnatinsa a kokarin da take yi na magance matsalar tsaro.
Shugaban ya bayyana haka ne yayin da wasu jami’an jam’iyun suke shan ruwa a Fadar Aso Rock tare da wasu manyan ‘yan kasuwa, inda ya ce, rashin tsaro shi ne babbar matsalar da ke damun kowane dan Najeriya.
Shugaban ya ce a makon jiya, yayin taron babban kwamitin gudanarwa na jam’iyyarsa ta APC, an fitar da kwakkwarar matsaya cewa jam’iyyar za ta ci gaba da kokarin karfafa turakun dimokradiyya a dukkan matakan mulki na kasa.
Ya kuma tabo batun saukaka kasuwanci a kasar inda ya shaida wa manyan ‘yan kasuwan da ke dakin cewa, gwamnatinsa ta taka rawar gani a fagn inganta yanayin kasuwanci a Najeriya, sannan ya bukaci su taimaka ma ta wajen kawar da talauci da samar da ayyukan yi ga matasa:
“Babu gwamnatin da ta yi aiki mai yawan namu a bangaren samar da daidaitaccen yanayi da renon kasuwanci ga manya da kananan kamfanoni domin su bunkasa.
Yayin da yake magana a madadin jam’iyyun siyasa da suka halarci shan ruwan, Injiniya Yusuf Yabagi, wanda shi ne shugaban jam’iyyar Action Democratic Party (ADP) ya bayyana shugaba Buhari a matsayin mai yekini gina dimokradiyya na gaske.
‘Yan kasuwan da suka halarci shan ruwan ma sun yi tsokaci, inda Mista Kola Adesina wada shi ne shugaban kamfanin Sahara Group, ya ce tilas shugaban da zai gaji Muhammadu Buhari “ya rungumi salon karfafa gwuiwar jama’ar kan samar da sabuwar Najeriya, ba gina kansa ba kawai.