Jam’iyyun adawa a Senegal sun yi fatali da shiga tattaunawar da shugaban ƙasar Macky Sall ya gabatar ta yin taron tsayar da sabuwar ranar zaɓen shugaban ƙasar bayan da ya sanar da ɗage zaɓen a farkon wannan wata.
Da alama dai rikicin siyasar ƙasar Senegal bai kare ba bayan da ƴan takarar shugaban kasa 16 daga cikin 19 na adawa suka ce ba za su shiga tattaunawar ba, wadda aka shirya gudanarwa a farkon mako mai zuwa.
Kungiyoyin farar hula da dama su ma sun yi fatali da batun tattaunawar.
Wannan ya biyo bayan jawabin da shugaba Macky Sall ya yi ta talabijin a daren ranar Alhamis, inda ya yi alƙawarin yin murabus a ƙarshen wa’adinsa, ranar 2 ga Afrilun 2024, sai dai bai bayyana sabuwar ranar da za a gudanar da zaɓen ba.
Mista Sall, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Abuja domin halartar wani babban taro na kungiyar ECOWAS, na fuskantar matsin lamba kan ya sanya sabuwar ranar zaɓe, tun bayan da majalisar ƙoli ta shari’a ta ƙasar ta bayyana ɗage zaɓen a matsayin haramtacce.
Yunƙurin ɗage zaɓen ya samu kakkausar suka daga ƙasashen duniya, waɗanda ke kallon Senegal a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashe masu tafiyar da mulkin dimokuradiyya kan tsari mai kyau, yankin da ake fama da juyin mulkin a yankin Yammacin Afirka.