Jam’iyyun adawa hudu a Najeriya sun shigar da ƙara domin ƙalubalantar nasarar zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata.
Dan Takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubkar da na LP Peter Obi da na AA Solomon Okangbuan da kuma na jam’iyyar APM Chichi Ojei duka sun shigar da ƙara gaban kotun ƙorafin zaɓe domin ƙalubalantar nasar Tinubu sa’o’i kafin cikar wa’adin da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba su dama na ƙalubalantar sakamakon zaɓen.
Manyan ‘yan takarar hamayyar biyu Atiku Abubakar da Peter Obi sun nemi kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen da ta ayyana cewa Tinubu bai ci zaɓen da aka gudanar ba.
Peter Obi ya yi zargin cewa an yi aringizon ƙuri’u a jihohin Rivers da Legas da Taraba da Benue da Adamawa da Imo da Bauchi da Borno da Kaduna da kuma jihar Plateau.
Obi na buƙatar kotun da ta ƙwace takardar shaidar cin zaɓe da hukumar INEC ta ba shi, tare da ba shi sabuwar takardar shaidar cin zaɓe.
Ranar Talata da yamma ne Amurka ta fitar da wata sanarwa tana mai Allah wadai da ƙaruwar razanar da masu kaɗa ƙuri’a da sauran laifukan zaɓe da ta ce an aikata a lokacin zaɓen gwamnoni na ranar 18 ga watan Maris.