Jagoran adawa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubaiar, ya yi kira ga jam’iyyun adawa a ƙasar su haɗa karfi da karfe a wuri ɗaya don tsamo dimokraɗiyyar ƙasar daga tsunduma zuwa mai bin jam’iyya ɗaya.
Ya kuma ja hankali a kan buƙatar yin hattara game da komawar Najeriya, tsarin jam’iyya ɗaya mai mulkin kama-karya.
Wata sanarwa da Paul Ibe, mashawarcin ɗan takarar shugaban ƙasar a zaɓen watan Fabrairun 2023 ya fitar ranar Talata, ta ce Atiku ya yi kiran ne lokacin da ya karɓi bakuncin shugabannin majalisar tuntuɓa tsakanin jam’iyyu ta Najeriya (IPAC).
Tsohon mataimakin shugaban Najeriyar, shi ne ya zo na biyu a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi a farkon wannan shekara, wanda Bola Tinubu ya kayar da shi.
A cewarsa, aikin kare mutuncin dimokraɗiyya a ƙasar, ba kawai na mutum ɗaya ba ne.
Ya nunar da cewa hakikanin gaskiya tsarin dimokraɗiyyarmu cikin sauri na komawa zuwa tsarin jam’iyya ɗaya, “kuma tabbas kun sani cewa idan tsarin jam’iyya ɗaya ne da mu, to kawai mu mance da maganar dimokraɗiyya”.
Atiku ya ƙara da cewa “Dukkanmu mun ga yadda jam’iyyar APC ke daɗa mayar da Najeriya zuwa ƙasar mulkin kama-karya mai jam’iyya ɗaya. Idan ba mu zo mun haɗu don kalubalantar abin da jam’iyya mai mulki take ƙoƙarin kafawa ba, dimokraɗiyyarmu za ta sha wahala, kuma sakamakon haka zai shafi hatta zuri’ar da ba a ma haifa ba”.


