fidelitybank

Jam’iyyu hudu sun narke sun koma goyon bayan Atiku

Date:

Kwanaki biyu bayan da jam’iyyar APM ta ruguza tsarinta na goyon bayan jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, wasu jam’iyyun siyasa hudu sun bi sahun gaba.

POLITICS NIGERIA ta rawaito cewa, an bayyana hakan ne a hukumance a ranar Asabar a taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a filin wasa na Ribadu da ke Jimeta-Yola a jihar Adamawa.

Jam’iyyun dai su ne Action Peoples Party (APP), Action Alliance (AA), National Rescue Movement (NRM), da kuma African Democratic Congress (ADC).

Da yake magana a madadin sauran shugabannin jam’iyyun siyasa na kasa, shugaban jam’iyyar APM na kasa, Yusuf Mamman Dantalle, ya ce jam’iyyun sun cimma matsayar daukar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ne saboda shi ne ya fi cancanta a cikin ’yan takara 18.

Sai dai ya ce jam’iyyun za su halarci zabukan gwamnoni, na kasa da na ‘yan majalisun jiha.

Wasu daga cikin jiga-jigan PDP da suka halarci gangamin Adamawa sun hada da gwamnoni Udom Emmanuel (Akwa Ibom), Aminu Tambuwal (Sokoto), Ahmadu Fintiri (Adamawa), Godwin Obaseki (Edo) da kuma Bala Mohammed (Bauchi).

Sauran sun hada da tsohon dan majalisar tarayya, Dino Melaye da Iyorchia Ayu, shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

nnn.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp